NCC za ta rufe layukan da ba a haɗa su da NIN ba a Satumba

Spread the love

Hukumar sadarwa ta ƙasa ta sanar da cewa duk layin wayar da ba a haɗa da NIN za ta rufe shi nan da 14 ga watan Satumba.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hukumar ranar 28 ga Agusta wanda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Rueben Maoka ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta fito bayan da hukumar ta ba da rahoton cewa tabbas an samu nasarar dokar domin kusan kaso 96% na ƴan Nijeriya sun haɗa layukan nasu da NIN.

Daga ƙarseh hukumar ta sanar da kamfanonin sadarwa cewa daga 15 ga Satumba 2024, duk wani layi da ba a haɗa shi da NIN a dakatar da shi domin haka shine doka.

By ukarofi