
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da buƙatar hukumar leƙen asiri (DIA) na tsare wani Mataimakin Sufuritandan ƴan sanda da wasu mutane 19 na tsawon kwana 30 kan zargin su da hannu acikin laifukan ta’addanci.
Mai Shari’a, Peter Lifu yayi hukuncin inda ya ce a tsare ASP A. A Babangida da waɗanda ake tuhuma don jami’an na DIA su samu damar gudanar da bincike mai zurfi akan su kan laifukan da ake zargin masu a kai.
Ana zargin jami’in ɗan sandan wanda aka kama tun a watan Yuni, 2024 ne da taimaka wa mayaƙan Boko Haram, masu garkuwa da mutane da kuma ƴan ta’addar ISWAP wajen gudanar da ayyukan su a wasu sassan Nijeriya.
Wanda ke wakiltar hukumar kan ƙarar, S. A Aminu ya nemi kotun ta ba su iznin tsare waɗanda ake zargin na tsawon kwana 90.
