NCDC ta gargaɗi ’yan Nijeriya kan amfani da namijin goro da sunan maganin Ebola 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka ta Nijeriya, ta gargaɗi ’yan Nijeriya da su guji amfani da namijin goro, ruwan gishiri, ganye, kuɓewa da sauran abubuwan da ba a tabbatar da su ba a matsayin maganin cutar Ebola ba.

A cikin wata sanarwar wayar da kai mai taken “Ebola: Tatsuniya Da Gaskiya,” hukumar ta ce yaɗa bayanan ƙarya da magungunan gida na iya ƙara firgici tare da kawo cikas ga matakan kariya daga cutar.

Sanarwar ta biyo bayan yaɗuwar jita-jita a shafukan sada zumunta bayan samun sabbin rahotannin cutar Ebola a wasu ƙasashen Afirka kamar Congo da Uganda.

Hukumar ta bayyana cewa duk da cewa ba a samu wani tabbataccen kaso na Ebola a Nijeriya ba, ƙasar na cikin shirin ko-ta-kwana saboda yawan zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe.

NCDC ta jaddada cewa babu wata hujjar kimiyya da ke nuna cewa namijin goro, ruwan gishiri ko wasu ganyaye na iya hanawa ko warkar da cutar Ebola.

Daraktan Janar na hukumar, Jide Idris, ya ce Nijeriya na cikin haɗarin shigo da cutar saboda yawan motsin jama’a da kuma wahalar gano alamomin cutar a matakin farko.

By ukarofi