NDLEA ta tsare ɗalibar jinya bisa safarar hodar iblis ta hanyar haɗiya

Spread the love

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta tsare wata ɗalibar jinya mai shekaru 26 da haihuwa a jami’ar Noida International da ke ƙasar Indiya domin gurfanar da ita a gaban kotu bisa zarginta da yunƙurin safarar hodar iblis ta hanyar haɗiye ƙulli 76.

Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

Babafemi ya ce wadda ake zargin tana yunƙurun haɗiye ƙullin hodar iblis ne, sa’o’i kaɗan kafin hawanta jirgin zuwa ƙasar Kudancin Asiya ta filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, MAKIA, Kano.

Ya ce, wadda ake zargin tana shirin tafiya birnin Delhi na ƙasar Indiya daga MAKIA Kano a cikin jirgin ƙatar Airways mai lamba 1432 a ranar Juma’a amma an kama ta a ɗakinta da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Alhamis.

“An kama ta ne a otel ɗin Royal Park da ke Sabon Garin Kano, a lokacin da take jiran jigilar hodar iblis da za ta haɗiye kafin tashinta da safe.

“An bankaɗo shirinta ne a lokacin da jami’an NDLEA da ke sintiri a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi, a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, suka kama wani dattijo mai shekaru 31 da haihuwa a cikin wata motar bas da ta taho daga Legas zuwa Kano.

“Cikin baƙar jakarsa akwai na’urar magana da sauti, wadda aka yi amfani da ita wajen bayyana yadda za a haɗiye ƙullin hodar iblis 76 masu nauyin kilogiram 1.340, wanda zai kai wa Esther a Kano.

“Sakamakon gaggawa da aka bi a Kano ya kai ga kama wata ɗalibar jami’ar jinya a ranar.”

A cewar Babafemi, ɗalibar aikin jinya ta yi ikirarin cewa ƙungiyar kwaya da take yi mata aiki ne ta ɗauko ta a ƙasar Indiya sannan ta biya ta kuɗin zuwa Nijeriya domin jin daɗin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

“Don gudun kada iyayenta su san tana Nijeriya, ba ta je jiharsu ta haihuwa ba, Imo, sai dai an ajiye ta na tsawon mako biyu a wani otal da ke Enugu, daga nan aka ɗauke ta zuwa Abuja.

“Daga nan ta yi tattaki daga Abuja zuwa Kano inda aka ajiye ta a otel din Royal Park domin ta haɗiye kwalayen hodar iblis 76 da aka aika mata daga Legas kafin ta hau jirgin ƙatar Airways zuwa Indiya a safiyar Juma’a.

“Ta ce an yi mata alƙawarin sama da dala 5,000 (Kimanin Naira miliyan 9) idan har ta samu nasarar kai haramtattun kayayyakin zuwa Indiya,” inji Babafemi.

By ukarofi