Hukumar shirya jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar kammala sakandire (SSCE External) na shekarar 2024.
Shugaban NECO, Farfesa Dantani Wushishi, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanar da sakin sakamakon a Minna ranar Juma’a.
A cewarsa, ɗalibai 57,114 ne suka samu maki mai kyau a Turanci da Lissafi, wanda ke wakiltar kashi 67.53% na wucewa.
Jimillar ɗalibai 86,067 ne suka zauna jarrabawar, inda aka samu raguwar aikata maguɗin jarrabawa.
Wushishi ya bayyana cewa an gwada ɗalibai a fannonin darussa 29, inda 83,220 suka rubuta Turanci, yayin da 83,024 suka rubuta Lissafi.
A cewarsa, ɗalibai 62,929 (75.62%) sun samu sakamako mai kyau a Turanci, yayin da 77,988 (93.93%) suka samu maki mai kyau a Lissafi.
Har ila yau, ɗalibai 70,711 (83.39%) sun samu maki mai kyau a darussa biyar ko fiye, ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba.
Sai dai, ɗalibai 6,160 aka kama da aikata maguɗin jarrabawa, adadin da ya ragu da kashi 27.7% idan aka kwatanta da 2023.
Bugu da ƙari, an bada shawarar hana malamai bakwai gudanar da jarabawa saboda gazawa wajen kulawa, jinkiri da taimaka wa ɗalibai wajen maguɗi. Malaman sun fito daga Oyo (2), Ogun (2), Lagos (1), Cross River (1), da Ebonyi (1).
Haka kuma, an soke cibiyoyi 14 da suka haɗa da 10 a Ogun da 4 a Oyo saboda aikata maguɗin jarrabawa gaba ɗaya a darussa tara.
Shugaban NECO ya bayyana cewa ɗalibai na iya duba sakamakonsu ta shafin NECO na yanar gizo, www.neco.gov.ng, ta amfani da lambar rajistar jarabawarsu.
Wushishi ya gode wa Gwamnatin Tarayya, Ministan Ilimi da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar.
Haka kuma, ya sanar da sakin sabon tsarin rarraba ma’aikatan NECO na 2025 ta hanyar shafin apcic.neco.gov.ng/myapc.