Za a yi alfahari da Hukumar NEDC bisa zuba jari a ilimi da fasaha – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce nan gaba za a yi alfahari da Hukumar Ci-gaban Shiyyar Arewa-maso-Gabas (NEDC) saboda ƙoƙarinta na faɗaɗa hanyoyin samun ababan ci-gaba na more rayuwa, wadda ta zuba jari a harkar ilimi da fasahar ‘green technology’ ta shirin ‘Accelerated Senior Secondary School’, wato ASSEP.

Ya bayyana shirin ASSEP a matsayin wani salo na dacewa da tafiyar zamani, ya na mai cewa ilimi shi ne abinda zai sa yaro ya zama abin alfahari acikin al’umma.

Shettima ya faɗi haka ne a ranar Alhamis, a yayin wani zama da tawagar gudanarwar NEDC a Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja, wadda ta gana da shi musamman don ba shi ba’asi game da ayyukan ASSEP.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce shiga harkokin ababan more rayuwa da hukumar ta yi abu ne mai kyau musamman a ASSEP da zuba jari a fasahar ta green tech, waɗanda za su taimaka wajen kawo gagarumin sauyi.

Har’ilayau, Shettima ya yaba da nasarorin da ASSEP ya samu, waɗanda a cewarsa za su taimaka wajen inganta harkokin karatu ga ɗalibai a zamanance.

Ya kuma yi kira ga hukumar da ta haɗa kai da masu-ruwa-da-tsaki don tabbatar da inganta ayyukansu.

A nasa jawabin, ƙaramin Ministan Ci-gaban Shiyya, Uba Maigari Ahmadu, ya ce an ƙirƙiro shirin ASSEP ne don bunƙasa harkokin karatun makarantun sakandare a shiyyar, wanda hakan wani ɓangare ne na babbar ajandar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta inganta harkar ilimi a Nijeriya.