Newcastle ta hana Haaland zura ƙwallon Premier League na 100 bayan doke City

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙoƙarin Erling Haaland na zura ƙwallon Premier League a Manchester City na 100 ya ci tura bayan da Newcastle United ta doke su da ci 2 da 1.

Haian ya sa City ta gaza rage adadin makin ratar da ke tsakanin ta da ta ɗaya a teburin, wato ƙungiyar Arsenal.

Da fari, Newcastle ce ta fara zura ƙwallo a ranar City ta ɗan wasa Harvey Barnes a minti na 63.

Saidai, nasarar ta samu ne na tsawon mintina biyar a lokacin da City ta farke ta hannun ɗan wasa Rúben Dias a minti na 68.

Jim-kaɗan bayan haka ne, hallau ɗan wasa Barnes ya sake maƙala wa Manchester ƙwallo a raga, wato ana saura minti 20 a tashi a wasan.

Duk da cewa, City ta yi ta ƙoƙarin ganin ta farke, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba.

By Babaji