Lewandowski ya zura ƙwallon farko a Camp Nou cikin shekara biyu bayan Barca ta lallasa Bilbao

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wasan farko da ta buga a filin wasa na Camp Nou tun bayan gyara shi, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta yi nasarar lallasa Athletic Bilbao da ci 4 da 0.

Hakan ya nuna Barca ta yi wasa 12 a gasar Laliga ba tare da an doke ta a ko ɗaya ba, inda ta yi nasarar a goma da yin canjaras a biyu.

Wannan shi ne wasa na farko a filin wasan da ƙungiyar ta yi nasara a tsawon sama da shekarq biyu.

Bayan minti huɗu da fara wasan ne ɗan wasan gaba Robert Lewandowski ya zura ƙwallo ɗaya a ranar Bilbao.

Daga bisani Ferran Torres ya ƙara ɗaya, wadda bayan dubawa, jami’an na’urar tantancewa ta VAR ta soke. Ana dab ta tafiya hutun rabin lokaci ne ɗan wasan ya sake nasarar zura ƙwallo, wanda hakan ya sa aka tafi hutun rabin lokaci a ci 2 da 0

A zagaye na biyu bayan minti uku da fara wasa sai Fermin Lopez ya zura ta uku. Lamarin da ya ƙara hefa Bilbao halin tsaka mai wuya.

A yanzu Bilbao ta sha kaye a wasanni huɗu da yin kunnen doki a ɗaya cikin wasanni biyar da ta buga.

By Babaji