
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Farfesa Wole Soyinka ya caccaki Shugaban Amurka Donald Trump bisa barazanar da ya yi na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya, yana mai bayyana kalamansa a matsayin abinda ke nuna rashin sanin tsauraran ƙalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta.
Gogaggen tauraron marubucin ya bayyana haka ne a ranar Jumma’a bayan ganawa da Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia a Makurɗi.
A cewar Soyinka, babu wani shugaba na wata ƙasa da zai tsoma baki a matsalolin tsaron Nijeriya ba tare yin fahimtar da ta dace ba game da sarƙaƙiyar da ke cikin al’amarin ba.
Ya soki Shugaba Trump akan zai kawo wa ƙasar ɗauki ba tare da yin karatun ta nitsu ba akan halin tsaro a Nijeriya.
Haka kuma Farfesan ya bayyana cewa, ayyana ire-iren matakan musamman na amfani da ƙarfi ka iya zama matsala ga ƙasar.
Ya ƙara da cewa, wajibi ne gwamnatoci su bada kariya ga ƴan ƙasa, sannan waɗanda ake kai wa hare-hare sun cancanci girmamawa.
A ƴan makonnin da suka gabata ne Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta bisa zargin yi al’ummar Kiristancin kisan kiyashi a ƙasar, lamarin da ya sa ya yi barazanar ɗaukar matakin soja.
