Wajibi ne ka yaƙi ƴan bindigar Fulani – Ɗan majalisar Amurka ga Tinubu bayan garkuwa da ɗalibai

Spread the love

Ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Riley Moore, ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta fuskantar ƙungiyoyin ƴan bindiga a yankin Arewa ta tsakiya.

Moore ya faɗi haka ne kwanaki kaɗan da sace yara sama da 300 da malamai 12 daga Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Jihar Neja a ranar Juma’a.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Moore ya bayyana ɓacin ransa kan harin da aka ruwaito, yana cewa: “A matsayina na uba, ganin irin waɗannan hare-hare yana tada min hankali ƙwarai.”

Ya kuma yi kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen yaƙar waɗanda ya zarga da aikata wannan tashin hankali, yana mai cewa gwamnati wajibi ne ta ƙwace makaman mayakan Fulani masu tsattsauran ra’ayi da ke razana Yankin Arewa ta Tsakiya.

Ɗan majalisar ya ƙara da zargin cewa tashin hankalin da ke fuskantar Kiristoci a Nijeriya na ƙara ta’azzara don haka wajibi ne a kawo ƙarshensa.

Ya yi kira da a ƙara haɗin-gwiwa tsakanin Abuja da Washington domin daƙile rashin tsaro, yana mai cewa “Gwamnatin Nijeriya ce ya rataya a wuyanta ta yi aiki tare da Amurka domin dakatar da kashe-kashe da sace-sacen ’yan uwanmu Kiristoci.”

Kazalika, Moore ya gargaɗi cewa cigaba da hare-haren ka iya haifar da ɗaukar mataki daga gwamnatin Amurka.

By Babaji