
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata tawagar al’ummar Musulmin Nijeriya ta ƙaddamar da kiran neman a dakatar da manhajar Netflix da ayyukanta bisa yaɗa fim ɗin ‘The Herd’.
Fim ɗin, wanda ke nuna yadda ake garkuwa da ƴan Nijeriya a yau da kullum daga Fulani makiyaya da ƴan bindiga, ya haifar da cecekuce acikin masu kallo musamman a kafar X inda ake ta kiraye-kirayen al’umma da su goge Netflix daga wayoyinsu.
Hakan yana nuni da yadda ake cigaba da fargaba game da yadda ake nuna ababen da ke faruwa musamman akan ƴancin yaɗa ayyukan fasaha da nauyin zamantakewa acikin al’umma.
A ranar 16 ga watan Nuwamba, 2025 aka fitar da fim ɗin wanda tauraron Nollywood, Daniel Etim-Effiong ya bada umarni, inda sama da mutane miliyan 30 suka kalla zuwa yanzu.
Fim ɗin ya nuna cewa a gaɓar farko ana nuna yadda al’umma ke zaune cikin farin ciki da annashuwa inda daga bisani aka ga yadda suke gudun nema tsira ga rayukansu.
