Ni da Chelsea mun zama abu ɗaya – Mourinho

Spread the love

Tsohon kocin ƙungiyar Chelsea ta Ingila, Jose Mourinho wanda yanzu yake horar da ƙungiyar Benfica ya ce shi da ƙungiyar ta Stanford Bridge sun zama hanta da jini.

Mourinho ya bayyana haka ne a ganawarsa da manema labarai kan shirye-shiryen da yake yi na jagorantar ƙungiyar Benfica ta ƙasar Portugal a wasan da za ta fafata da Chelsea na gasar zakarun turai a Ingila a ranar Talata.

Sai dai ya ce a lokacin da ake tsaka da wasan, “zan jingine ƙaunar da yake yi wa Chelsea na minti 90 domin in fuskanci aikin da nake yi wa ƙungiyar Benfica.”

Ya ce, “a ƙungiyar Chelsea na zama abin da na zama, har ake magana, sannan ni ne na ɗaga darajar Chelsea ta zama babbar ƙungiyar da a yanzu ake ji da ita. Tarihina ba zai taɓa cika ba ba tare da ambaton Chelsea ba, haka kuma ba a taɓa raba tarihin ƙungiyar da ni ba.”

Jose ya ƙara da cewa, yana matuƙar ƙaunar ƙungiyar, amma “a yau aikina shi ne jagorantar Benfica ta samu nasara.”

By ukarofi