
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu akan iƙirarinsa na cewa da ba dan shi ba marigayi Muhammadu Buhari ba zai ci zaben 2015 ba.
Amaechi ya ce, Tinubu, wanda tsohon gwamna ne kima jagora a jam’iyyar APC, bai yi abin a zo a gani ba a zaman Buhari shugaban ƙasa.
Amaechi ya ce bai kamata Tinubu ya ce shi ne ya yi silar zaman Buhari shugaban kasa a 2015 ba, har ma ya riƙa iƙirari da cewa tallafin siyasarsa ne ya sa Buharin ya zama.
Cikin bayanan kalubalen na Amaechi, ya ce nasarar Buhari nasara ce da ta samu ta hanyar hadaka da hadin gwiwa daga manyan ‘yan siyasa da dama ba ta mutum daya tal ba.
Amaechin ya bayyana haka ne a wani shirin gidan talabijin na Arise, inda ya ƙara da cewa tare da shi aka yi hidimar yaƙin zaɓen Buhari, wanda a lokacin ne ma ya jagoranci ayari da dama na magoya bayan Buhari a wancan lokaci har aka samu nasara.
A yayin zaɓen 2023 ne Shugaba Tinya yi iƙirarin, inda a lokacin ne ya ce lokacin da zai mulki Nijeriya ya yi don haka damarsa ce.
