
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Lahadi Shugaba Bola Tinubu zai karɓi takardar shaidar zama ɗan takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APC, bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar domin zaɓen 2027.
Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga a wata sanarwa ta ranar Asabar, ya ce Kwamitin Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Ƙasa na APC ne zai miƙa takarda da tutar a Cibiyar Taro ta Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja.
Ya ce, hakan zai gudana ne bayan tattara sakamakon zaɓen daga sassan ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar.
Sanarwar ta kuma ce, gwamnonin APC, mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar ne za su halarci taron.
Ana kallon wannan mataki a matsayin wata muhimmiyar alama ta fara shirin APC gabanin babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke cigaba da kusantowa.
