
Shahararren malamin addinin Musuluncin nan da ke zama a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya fitar da gargaɗi mai ƙarfi ga mutanen da ke cigaba da alaƙanta shi da ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a ƙasar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa, shehin ya nuna ɓacin ransa akan yadda wasu ke amfani da kalaman ɓatanci wajen shafawa da’awarsa kashin kaza, inda ya buƙaci masu sukarsa da su gaggauta dakatawa.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa, ɗaukacin ƙoƙarin da ya yi a baya na shiga daji domin tattaunawa da ƴan bindigar ba don yana goyon bayan ayyukansu ba ne, illa dai wani mataki ne na neman sulhu da kuma fahimtar dabarun da za su kawo ƙarshen zubar da jini.
Ya ƙara da cewa, iƙirarin da wasu ke yi na cewa yana da alaƙa ta sirri ko ta kasuwanci da miyagun mutanen labarin cin kanzon kurege ne, domin babban burinsa a kowane lokaci shi ne ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a fadin shiyyar Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.
A cikin bayanin nasa, malamin ya jaddada cewa kalaman da masu sushin ke yaɗuwa da su a kafafen sada zumunta na zamani barazana ce ga tsaron lafiyarsa, kuma hakan yana raba kan al’umma a maimakon a nemi hanyoyin gyara.
A ƙarshe, ya yi kira ga jami’an tsaro da su mayar da hankali wajen kamo ainihin miyagun da ke addabar al’umma maimakon fuskantar mutanen da ke bayar da shawarwari na gaskiya domin fita daga cikin wannan matsala.
