Nijar: ‘Yan Nijeriya mazauna iyaka na zargin jami’an tsaro suna muzguna musu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu mazauna unguwar Magamar Jibiya dake kan iyakar Nijeriya da Nijar a jihar Katsina, sun zargi jami’an tsaro da ɗaukar su kamar ‘yan Nijar.

Mutanen sun yi wannan zargin ne a wata tattaunawa da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Katsina ranar Talata.

Sun yi iƙirarin cewa jami’an Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) da ba a san ko su waye ba ne ke tauye haƙƙinsu a kullum.

A cewar Ɗayyabu Muhammad, jami’an tsaro da ke kan hanyar Katsina zuwa Jibiya a kodayaushe suna bin su a duk lokacin da suka ga suna jigilar hatsi da aka sayo daga Katsina don amfanin kansu.

“A duk lokacin da muka sayi hatsi, musamman masara, jami’an tsaro, musamman hukumar Kwastom, suna tare mu a kan hanyarmu ta zuwa yankunanmu da ke kusa da kan iyaka.

“A mafi yawan lokuta, nakan kashe fiye da Naira 12,000 kafin in isa gida a duk lokacin da nake jigilar kayan da aka sayo don ci a cikin al’ummarmu.

“Waɗannan jami’an tsaro suna da shingayen bincike kusan 37 daga Katsina zuwa Jibiya, wanda bai wuce kilomita 47 ba.

“Kuma a kowane shingen bincike, dole ne su karɓi kuɗi a wurinmu, wanda abin takaici ne.

“A matsayinmu na ‘yan Nijeriya, ba za mu iya siyan kayan abinci daga birni mu kai su ga danginmu ba tare da muzgunawa ko ƙwace ko kuma a kama kayan ba,” inji shi.

Muhammad ya ce mutanensu ba sa cin moriyar dimokraɗiyya.
Ya yi nadamar cewa suna rayuwa ne a cikin hare-hare na yau da kullum daga ’yan fashin daji waɗanda suka sa rayuwar al’ummar yankin cikin fargaba.

Wani mazaunin yankin Alhaji Abdullahi Musa ya yi zargin cewa jami’an tsaro a yankinsu ba sa ba su kariya daga hare-haren ‘yan bindiga.

“Duk lokacin da aka kai harin ‘yan bindiga, da wuya su zo a lokacin da ya dace,” inji shi.

“Duk da yawan wuraren binciken ababen hawa, ‘yan fashin sun samu hanyar zuwa su kai mana hari,” inji shi, ya ƙara da cewa a ko da yaushe a bar su.

“Ku yi tunanin kawai, ba za su iya kare mu ba amma za su iya tursasa mu yayin jigilar kayayyaki don ci a cikin al’ummarmu.

“Ba mu kai su Jamhuriyar Nijar ba.
“Idan har suna ƙoƙarin hana safarar kayayyaki zuwa Nijar, to su toshe kan iyaka.
“Sun kuma san duk hanyoyin da suka saɓa wa doka, waɗannan wuraren ne ya kamata su tare, ba hanya ba.

“Rufe iyakokin ya shafe mu da gaske saboda yawancin kasuwancinmu a nan sun dogara ne da goyon bayan ‘yan Nijar,” inji Musa.

Ya ci gaba da cewa, kafin a rufe iyakar, yana da jarin sama da Naira miliyan biyu, amma ba shi da kobo a halin yanzu.

Ya ce wahalhalun da al’umma ke fuskanta a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon rufe iyakokin da aka yi, lamarin da ya jawo durqushewar tattalin arzikin yankin.

“Kuma, abin takaici, sama da kashi 90 na manoman mu ba sa noma saboda rashin tsaro.

“Muna fuskantar yunwa sosai da kuma lokuta masu wahala.

“’Yan siyasar mu ba sa taimakawa al’amura, suna zuwa wurinmu ne kawai a lokacin da suke buƙatar ƙuri’unmu, amma da ƙyar mu sake ganinsu bayan zaɓe.

Wani mai sayar da kayayyakin gyara a yankin, Alhaji Abubakar Muhammad ya ce ya rufe kasuwancinsa ne saboda rashin samun tallafi.

Muhammad ya ce, “Mafi yawan kwastomomi na sun fito ne daga jamhuriyar Nijar da sauran al’ummomin da ke kewaye, amma rashin tsaro ya hana su zuwa.

Don haka jama’a sun yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da hukumomin tsaro da ‘yan siyasa da su kawo musu ɗauki domin ganin an magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.

Da yake mayar da martani kan zargin, Kakakin Hukumar NCS a Jihar, CS Tahir Balarabe, ya shawarci mazauna garin da su kai rahoton duk wani jami’in da ke neman kuɗi a wurinsu.

Balarabe ya ce, “Rundunar ta na iyakacin ƙoƙarinta wajen tsaftace ayyukanta, kuma a shirye take ta tunkari duk wani jami’inta da aka samu da buƙata.