Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatocin Nijeriya da Turkiyya sun rattaba hannu kan wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) domin ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangaren ma’adanai masu ƙarfi, a wani yunƙuri na bunƙasa alaƙar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin Ministan Raya Ma’adanai Masu ƙarfi na Nijeriya, Dele Alake, da Ministan Makamashi da Albarkatun ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar, a gefen Taron Albarkatun ƙasa na Istanbul (INRES).
A cikin wata sanarwa da Mataimakiyarsa ta Musamman, Lara Owoeye-Wise, ta fitar ranar Litinin, Alake ya bayyana cewa Nijeriya na shirye ta yi amfani da ci gaban fasaha da ƙwarewar Turkiyya wajen binciken ma’adanai, horaswa, tsarin fasahar zamani, bayar da lasisi da bunƙasa ƙwarewar ma’aikata domin saurin aiwatar da gyare-gyare da ci gaban ɓangaren ma’adanai.
Ministan ya ce, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da cikakken goyon baya ga ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu musamman a fannonin ma’adanai da makamashi.
“Nijeriya a buɗe take wajen yin aiki tare da gwamnatin Turkiyya domin ƙarfafa tsarin shugabanci, haɓaka ƙwarewar fasaha da kuma bunƙasa harkar haƙar ma’adanai cikin tsari mai ɗorewa,” inji Alake.
Ya ƙara da cewa, sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta aiwatar a ɓangaren ma’adanai sun sauya yanayin gudanar da harkokin tare da janyo hankalin masu zuba jari na gaskiya.
Alake, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Dabarun Ma’adanai ta Afirka, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki matakai domin tsaftace ɓangaren, sauƙaƙa harkokin kasuwanci da samar da abubuwan ƙarfafawa ga masu zuba jari na ƙasashen waje masu sha’awar kafa haɗin gwiwa na dogon lokaci a Nijeriya.
A nasa ɓangaren, Ministan Makamashi da Albarkatun ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar, ya bayyana sabon haɗin gwiwar da Nijeriya a matsayin mai muhimmanci kuma mai dacewa da wannan lokaci.
Ya ce tsaron makamashi na duniya yanzu yana buƙatar ƙarin haɗin kai da alaƙa mai ƙarfi tsakanin ƙasashe.
Bayraktar ya yaba wa gwamnatin Nijeriya kan gyare-gyare da tsare-tsaren da ta fara aiwatarwa a ɓangaren ma’adanai, yana mai cewa kamfanonin Turkiyya na da sha’awar zuba jari a Nijeriya.
