Arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.89 a farkon 2026, inji NBS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya samu bunƙasa da kashi 3.89 cikin ɗari a farkon shekarar 2026 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahoton GDP na farkon shekarar 2026 da ta fitar ranar Litinin, 25 ga watan Mayu.

A cewar NBS, wannan ci gaba ya zarce kashi 3.13 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2025, sai dai ya yi ƙasa da kashi 4.07 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2025.

Hukumar ta ce ɓangaren noma ya samu bunƙasa da kashi 3.15 cikin ɗari a farkon shekarar 2026, idan aka kwatanta da ƙaramin ci gaban kashi 0.07 cikin ɗari da aka samu a daidai wannan lokaci na 2025.

Haka kuma, ɓangaren masana’antu ya samu ci gaba da kashi 3.50 cikin ɗari, wanda ya fi kashi 3.42 cikin ɗari da aka samu a shekarar da ta gabata.

Sai dai ɓangaren ayyuka ya samu bunƙasa da kashi 4.31 cikin ɗari, wanda ya ɗan ragu daga kashi 4.33 cikin ɗari da aka samu a rubu’in farko na 2025.

Rahoton ya nuna cewa ɓangaren ayyuka ne ya fi bayar da gudunmawa ga jimillar GDP ɗin ƙasar, inda ya bayar da kaso 57.73 cikin ɗari a farkon shekarar 2026, idan aka kwatanta da kaso 57.50 cikin ɗari na shekarar 2025.

NBS ta bayyana cewa jimillar GDP ɗin Nijeriya a farashin yau da kullum ta kai tiriliyan N110.79 a farkon shekarar 2026.

Hukumar ta ce, wannan ya fi tiriliyan N94.051 da aka samu a farkon shekarar 2025, wanda ke nuna bunƙasar da ta kai kashi 17.79 cikin ɗari.

A ɓangaren mai kuwa, NBS ta ce an samu bunƙasa da kashi 2.57 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wanda ya fi kashi 1.87 cikin ɗari da aka samu a farkon shekarar 2025.

Sai dai hukumar ta ce ci gaban ɓangaren mai ya ragu idan aka kwatanta da ƙarshen shekarar 2025, inda aka samu kashi 6.79 cikin ɗari.

A tsarin rubu’i zuwa rubu’i, ɓangaren mai ya samu bunƙasa da kashi 9.31 cikin ɗari a farkon shekarar 2026.

Rahoton ya nuna cewa ɓangaren mai ya bayar da kaso 3.92 cikin ɗari ga jimillar GDP ta haƙiƙa, wanda ya ɗan ragu daga kaso 3.97 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2025, amma ya fi kaso 2.87 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2025.

Hukumar ta kuma bayyana cewa matsakaicin yawan ɗanyen man da Nijeriya ta riƙa haƙowa a kullum a rubu’in farko na 2026 ya kai ganga miliyan 1.55 a rana, ƙasa da ganga miliyan 1.62 da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2025.

NBS ta ƙara da cewa ɓangaren da ba na mai ba ya bayar da kaso 96.08 cikin ɗari ga GDP ɗin ƙasar, wanda ya fi kaso 96.03 cikin ɗari da aka samu a shekarar da ta gabata.

A cewar hukumar, manyan ɓangarorin da suka taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin da ba na mai ba sun haɗa da sadarwa da fasahar zamani, noma musamman noman amfanin gona, kasuwanci, masana’antar siminti, harkokin kuɗi da inshora, gidaje, gine-gine da sufuri ta hanya.

By ukarofi

Leave a Reply