Tsadar gas ta tilasta wa talakawa amfani da itace da gawayi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Masu Kasuwancin Iskar Gas Ta Nijeriya (NALPGAM), ta bayyana damuwa kan ƙarancin iskar gas ta girki da kuma tashin farashinta a sassa daban-daban na ƙasar nan.

ƙungiyar ta ce, farashin gas ɗin ya tashi daga kusan naira 1,300 zuwa fiye da naira 1,500 kan kowanne kilo, gwargwadon yankin da ake saye.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, ta jawo hankalin Gwamnatin Tarayya, hukumomin gwamnati, masu kula da harkokin makamashi, masu shigo da gas, masu samar da shi, masu ajiyar gas a tankuna da kuma jama’a baki ɗaya kan abin da ta kira “rashin daidaiton samar da gas da tashin farashinsa” a faɗin ƙasa.

ƙungiyar ta bayyana cewa masu kasuwancin gas na biyan tsakanin naira miliyan 25.2 zuwa naira miliyan 26.2 domin sayen tan 20 na gas, gwargwadon wurin da ake saye.

Ta ce, abin takaici ne yadda ’yan Nijeriya suka wayi gari suna sayen gas ɗin girki, wanda ya kamata ya kasance kayan more rayuwa mai sauƙin samu, a farashi mai tsanani da ya zarce naira 1,500 kan kilo.

“Idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, akwai yiwuwar jama’a su fara nuna fushinsu ga masu gidajen sayar da gas,” inji sanarwar.

ƙungiyar ta ƙara da cewa, hauhawar farashin ya jefa miliyoyin gidaje, ƙananan ‘yan kasuwa, masu sana’ar girki da iyalai masu ƙaramin ƙarfi cikin matsananciyar wahala, kasancewar su ne suka fi dogaro da gas wajen gudanar da rayuwa ta yau da kullum.

NALPGAM ta bayyana cewa matsalar na iya rusa ci gaban da gwamnati ta samu wajen yaɗa amfani da makamashi mai tsafta a Nijeriya.

ƙungiyar ta kuma bayyana cewa mambobinta na fuskantar ƙalubale wajen samun gas saboda ƙarancin kayayyaki, tsadar farashi a ma’ajiyu, matsalolin sufuri da kuma hauhawar kuɗin gudanar da kasuwanci.

A cewarta, ko inda ake samun gas ɗin ma, ana sayar da shi ne a farashin da talakawan Nijeriya ba za su iya ɗauka ba.

Ta ce wannan matsala na barazana ga ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi wajen ƙarfafa amfani da gas a matsayin madadin kananzir, gawayi da itacen girki domin kare lafiya da muhalli.

ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa iyalai da dama na komawa amfani da itace da gawayi saboda tsadar gas, lamarin da ka iya ƙara lalata muhalli da sare bishiyoyi.

Har ila yau, NALPGAM ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar za ta iya haddasa ƙarin tashin farashin abinci, durƙushewar ƙananan sana’o’in gas, rasa ayyukan yi da kuma rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari a fannin makamashi mai tsafta.

By ukarofi

Leave a Reply