Daga MUHAMMADU MUJITABA a KANO
An bayyana cewa Nijeriya na buƙatar kyakkyawar zuma don amfanin al’umarta sama da Ton 100,000 a duk shekara kamar dai yadda Shugaban kamfanin samar da zuma a Nijeriya, Alhajii Aminu Musa Madurasa ya shaida wa manema labarai a Kano a farkon makon nan. Aminu Madurasa, ya ƙara da cewa a nan Nijeriya za a iya samun zuma sama da buƙatun ‘yan ƙasar nan a duk shekara, amma abun takaici shi ne, Nijeriya na iya samar da Ton 10,000 ne kacal a Najeriya a shekara sakamakon rashin tsaro, inda ya ce wanan ya sa an samu ƙarancin zumar a Najeriya.
Alhaji Shazali, ne mai matsayin manaja ne a kamfanin zumar, shi ma ya bayyana zuma da cewa wata kadara ce mai daraja da ya kamata gwamanti ta ba manoman zuma tallafi da tsaro don samar da wadatacciyar zuma da ɗaukacin abun da ake nomawa Nijeriya don ci gaban ƙasarmu.
