Daga DAUDA USMAN a Legas
Wani matashi mai suna Barista Lawal Ahmed UPE a Funtuwa ta jihar Katsina kuma jigo a tafiyar matasan jam’iyyar NNPP a jihar, ya shawarci matasan Funtuwa da na jihar Katsina da ma na ƙasar nan baki ɗaya da su ƙara ƙoƙari kuma su kasance masu neman ilimin boko da na Islamiyya tare da koyon sana’o’in dogaro da kai a Nijeriya baki ɗaya.
Barista Lawan Ahmed UPE Funtuwa ya yi wannan tsokaci ne a Funtuwa a lokacin da yake karɓar baƙuncin waɗansu gungun matasan jam’iyyar NNPP na jihar Katsina da kewayenta da suka kawo masa gaisuwar ban girma tare da neman shawararsa game da harkokin siyasar jam’iyyar NNPP a jihar Katsina.
Barista Lawan Ahmed UPE Funtuwa bayan ya kammala karɓar baƙuncin manyan bakinsa na matasan jihar Katsina ya ci gaba da shawartar matasan da su cigaba da gudanar da harkokin siyasar jam’yyar NNPP a cikin tsafta da mutunta junansu sannan kuma su kaucewa yin siyasar karɓar kuɗi a hannun ‘yan siyasa masu neman muƙamai na kujerun siyasa daban-daban na ƙasar nan domin samun ingattattun shuwagabanni waɗanda za su jagorancesu kuma su kawo masu ci gaban yankunansu da jihohinsu da ma ƙasar bakiɗaya.
UPE ya ci gaba da cewa haka zalika kuma matasan su gujewa yin siyasar banga domin kare mutuncin kansu da siyasarsu a Funtuwa da jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa to idan aka samu matasa da sauran al’ummar ƙasar nan suka tsayu a kan hakan to babu shakka Nijeriya za ta ƙara samun nasarori na zaman lafiya dama farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar bakiɗay.
Haka kuma UPE ya cigaba da shawartar ‘yan siyasa masu madafun iko na ƙasar nan baki ɗaya da su ƙara ƙoƙari a wajen kawo wa ‘yan mazaɓun yankunansu ayyukan cigaba da kuma yi wa al’ummarsu jagoranci mai kyau a cikin adalci domin kamanta sauke nauyin shugabancin da Allah Ubangiji ya ɗora masu da kuma neman samun ƙetare babban siraɗi a ranar gobe kiyama.
