Daga UMAR GARBA a Katsina
A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na inganta ɓangaren samar da abinci gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta kashe fiye da Naira bilyan 30 don inganta harkar noma.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan dawowarsa daga hutun wata daɗa da ya yi a ƙasashen waje.
A yayin hutun na shi Raɗɗa, ya kai ziyarar aiki a ƙasar Sin don duba hanyoyin haɓɓaka harkokin noma a jihar Katsina.
Gwamnan ya ce, za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen ne wajen kafa cibiyoyin sarrafa kayan gona a kowace ƙaramar hukuma.
A cewarsa, cibiyoyin za su horar da manoma dabarun noma na zamani tare da samar musu da kayan aikin noma, ta yadda manyan manoma da ƙanana za su samu damar mallakar kayayyakin aikin gona na bai ɗaya.
“Ba za ka iya bunƙasa jihar da kashi 90 cikin 100 na al’ummarta manoma ne, ba tare da zuba jari a harkar noma ba.
“Don haka, a ƙarƙashin tsarin, za a samar da cibiyoyi da za su samar da taraktoci na zamani, na’urorin girbi, ingantaccen iri, da dai sauran kayayyakin da ake buƙata,” inji shi.
Da yake bayani game da halin matsin rayuwa da al’uma ke ciki, Raɗɗa ya amince da halin ƙuncin tattalin arziƙin da ƙasar ke fama da shi.
Saboda haka ne ya buƙaci al’ummar jihar da su yi haƙuri, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na ƙoƙarin ɓullo da sabbin matakai don rage raɗaɗin talauci.
Gwamnan ya ce zai zagaya shiyoyi uku na jihar domin samun bayanai daga wurin jama’a don sanin irin aiyukan da suke so gwamnatinsa ta yi masu.
Da yake magana game da rashin tsaro, gwamna Raɗɗa ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ɗaukar ƙarin jami’an tsaron al’uma na jihar wato ‘Katsina Community Watch Corps’ tare da tura su wasu ƙananan hukumomin jihar domin inganta tsaro.
