Nijeriya ta fitar da jerin masu ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta fitar da jaddawalin sunayen mutane da ƙungiyoyi guda 48 da ake zargin su da hannu a ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

A ranar Asabar aka fitar da jaddawalin ƙarƙashin jagorancin Kwamitin Yanke Hukunci na Kasa (NIGSAC).

Jaddawalin ya ƙunshi sunayen mutane da ƙungiyoyi da ake zargin su da hannu a ayyukan da suka shafi ta’addanci.

Daga cikin waɗanda aka zayyano akwai ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Ansaru da kuma Islamic State West Africa Province, wato ISWAP.

Ga jerin su nan kamar yadda kwamitin ya wallafa:

By Babaji