
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta tsare wasu jami’an gwamnatin Jihar Kano kana daga bisani ta bayar da belinsu bayan da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ƙorafinsu akan zargin cin fuska da ɓata masa suna a Soshiyal Mediya.
An ruwaito cewa an gayyaci jami’an, inda aka yi musu tambayoyi har na tsawo sa’o’i huɗu kafin aka sallame su ɗaya bayan ɗaya, wanda ke nuna bincike akan al’amari zai cigaba da gudana.
Rahotanni sun nuna cewa tun da fari ƙungiyar Kwankwasiyya reshen Jihar Kano ce ta shigar da ƙorafi kan wasu jami’an gwamnatin, bisa zargin ɓata sunan shugabanninta da suka haɗa da sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Aminu Abdulsalam Gwarzo da Sanata Rufa’i Sani Hanga da sauransu.
Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tabbatar da al’amarin a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce, shi da wasu mutum uku da suka haɗa da Salisu Yahaya Hotoro, Ibrahim Adam da Hon. Nuhu Dambazau, an tsare su na wasu sa’o’i a hannun DSS bisa zargin aikata laifukan ɓata suna a kafafen sada zumunta.
Ya ƙara da cewa sun shafe sa’o’i huɗu a tsare kafin daga bisani aka sake su bisa beli.
Haka kuma ya bayyana cewa ana sa ran Sanata Kwankwaso zai kai wannan batu gaban kotu domin cigaba da shari’a.
A cewar Sanata Kwankwaso, al’amarin cin mutuncinsa ta kafar sada zumunta tsananta a ‘yan kwanakin nan musamman ganin yadda amfani da fagen wajen yaɗa saƙonnin ɓatanci ya zama ruwan dare.
