Nijeriya ta zaftare biliyan N10 na halartar taron ɗumamar yanayi na duniya

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta zaftare Naira biliyan 10 a taron ɗumamar yanayi da yake zuwa a ƙasar Azerbaijan.

A wata ganawa da manema labarai da mai ba shugaban ƙasa shawara a harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya faɗa ya bada tabbacin faruwar hakan ga taron da za ai kwana 11 a na yi.

“Ƴan Nijeriya da yawa za su iya tunawa shugaba Tinubu da gwamnatin tarayya a taron bara, yawan mutanen da su ka tafi dasu ya tada ƙura.

Domin haka, gwamnatin ta ɗauki matakin rage yawan mutanen da za su halarci taron, gudun abinda ya faru a bara a ƙasar Dubai kar ya maimaita kan shi.

Ya bayyana cewa wasu kwangiloli da aka bayar an lura ba su da amfani, don haka a wannan shekarar ba za ai irin wannan ba domin majalisar ƙasa ta ɗumamar yanayi za ta ɗauki nauyin wannan.

Ya cigaba da bayyana cewa, bayan bincike, an gano akwai jami’an gwamnati da zuwan su bashi da amfani, don haka wannan shekarar an ɗauki matakin daƙile wannan.

Saboda wannan, shugaban ƙasa ya bada umarnin bincike mai zurfi domin tabbatar da abunda ya faru domin gudun faruwar haka a gaba.

Bayan wannan bincike, ofishin jakada na musamman a kan taron wanda nake jagoranta tare da shugaban majalisar ɗumamar yanayi na ƙasa Nkiruka Madukwe mun yi wannan aiki, kuma mun ga abinda ya faru a taron COP28 kuma mun ɗauki matakai da zai hana faruwar haka a taron bana na COP28.

A dalilin wannan aiki, mun yi nasarar zaftare Naira biliyan 10 na kuɗin kashewa wanda wannan abun alfahari ne ganin yadda a ke fama da matsin tattalin arziki a ƙasar

By ukarofi