
Mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima, a yau ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban ƙasar Tanzaniya, Jakaya Mrisho Kikwete, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Tsohon shugaban ƙasar na Tanzaniya, ya zo Najeriya ne domin halartar bikin yaye ɗalibai ƴan rukuni na 32 na kwalejin nazarin ayyukan tsaro ta ƙasa, NDC.
A yayin ganawar tasu, Shettima yayi kira kan buƙatar ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa a tsakanin Najeriya da ƙasar Tanzaniya domin cigaban ƙasashen biyu.
Cikin jawabinsa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, wannan ya zama wajibi tun bayan alaƙar da ke akwai tsakanin Najeriya da Tanzaniya tuntuni a tarihi, musamman ta fuskar yaƙi da danniya da mulkin mallaka.
“Abu ne mai muhimmanci a yanzu ƙasashen su ƙarfafa tsare-tsarensu na tattalin arziƙi musamman ma ta fuskar cinikayyar kasuwanci cikin Afrika”, inji Kashim.
