Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na tabbatar da tsaro a shiyyoyi da nahiyoyi, inda ta buƙaci ƙasashen Afirka da su haɗa kai wajen tunkarar barazanar da ake fuskanta tare da samar da zaman lafiya.
Babban Hafsan Tsaron Nujeriya, Janar Christopher Musa ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan babban taron manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Afirka da za a yi a Abuja, wanda aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 25 zuwa 27 ga watan Agustan 2025.
Taron mai taken “Yaƙi da Barazanar Zamani da Tsaro a Afirka: Matsayin Haɗin Kai”, zai tara manyan hafsoshin tsaro daga ko ina cikin nahiyar don samar da hanyoyin warware matsalolin tsaro da Afirka ke fuskanta.
Janar Musa ya ce, Nijeriya na jagorantar ƙoaarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shugabannin sojojin ƙasashen Afirka, inda ya yi nuni da yadda ƙasar ke gudanar da ayyukanta na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar, da tallafa wa ƙasashen da ke fama da rikici, da kuma bayar da gudunmawar wanzar da zaman lafiya a duniya.
Yayin da barazanar tsaro ke ƙara ta’azzara a fazin Afirka, ya jaddada buƙatar haɗin kai a tsakanin ƙasashe domin gano ƙalubale tare da bayar da shawarwari masu ɗorewa.
“Ana kallon haɗin gwiwar a matsayin nuna goyon baya mai ƙarfi daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da al’ummar Nijeriya, sanin cewa yaƙin da ake yi yana buƙatar fiye da aikin soja kawai, yana buƙatar haɗin kai da shugabanni, ɗaukacin gwamnati da al’umma baki ɗaya don tabbatar da zaman lafiya da tsaro,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “a bisa dabaru, shirin na neman inganta musayar bayanan sirri, horar da haɗin gwiwa, da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka.”
Babban hafsan tsaron ya ci gaba da bayanin cewa taron zai ƙarfafa hanyoyin zaman lafiya da tsaro na ƙungiyar Tarayyar Afirka, kamar rundunar ECOWAS, tare da haza sabbin kamfanoni masu zaman kansu cikin dabarun tsaro.
“Daga ƙarshe, manufar Nijeriya ita ce kafa wani dandali da ‘yan Afirka za su tattauna tare da magance matsalolinsu, tare da ƙarfafa ƙa’idar cewa za a fara bayar da agaji daga gida,” inji shi.
A cewar masu shirya taron, an gayyaci dukkan ƙasashen Afirka 54 zuwa taron, inda sama da kashi 90 cikin ɗari suka tabbatar da halartar taron.
