Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Nijeriya makamai wanda kuɗinsu ya kai Dala miliyan 346. Ma’aikatar Harkokin Tsaron Amurkar ta ce, makaman da za a sayar wa Nijeriyar sun haɗa da manyan boma-bomai da kuma rokoki.
Ta ce, sayar da makaman zai ƙara inganta ɓangaren tsaron Nijeriya da kuma taimaka wa tsarin harkokin wajenta a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka.
“Cikin makaman har da wasu rokoki na zamani sama da 5,000,” inji sanarwar Washington. Ta bayyana cewa, Nijeriya ta buƙaci sayen makaman 1,002 MK-82 na bai-ɗaya na bom ɗin 500 lb, 1,002 MɗU-650 Air Foil Groups (AFGs), 5,000 Advanced Precision Kill Weapon System II, high-eɗplosive warhead tare da kuma motar roka ta MK66-4 da sauransu.
Amurka ta amince da sayar da kayan aikin soji da suka haɗa da jirage masu saukar ungulu 12, da abubuwam sarrafa makami na zamani guda 2,000, da na’urar ɗaukar hoton dare da darajarsu ta kai dala miliyan 997 ga Nijeriya a shekarar 2022.
DSCA ta kira masu kwangilar sayarwa a matsayin Lockheed Martin, RTɗ missiles and Defense (RTɗ.N), da BAE Systems (BAES.L).
Lockheed sananne ne wajen samar da na’urori masu cin gashin kansu, jiragen sama, makamai masu linzami, rokokin sararin samaniya, da dai sauran kayan tsaro.
Wasu daga cikin muhimman samfuransa sun haɗa da jirgin yaƙi na F-35 Lightning II, jirgin sama na C-130 Hercules, tsarin makami mai linzami na Patriot, da fasahohin kariyar makamai masu linzami daban-daban.
A 2014 lokacin mulkin Barack Obama, Amurka ta ƙi amincewa ta sayar wa Nijeriya wasu muggan makamai, bayan nuna damuwa kan zargin sojojin ƙasar da take haƙƙin ɗan adam.
A lokacin, gwamnatin Nujeriya ta yi ƙorafin cewa hakan na yin cikas a yaƙi da take yi da masu iƙirarin jihadi a Arewa maso Gabas.
