Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin African Industries Group ya sanar da shirinsa na kafa mafi girman kamfanin sarrafa ƙarafa da ke amfani da makamashin hasken rana a yankin Afirka da ke Kudu da Hamadar Sahara, bayan da Gwamnatin Jihar Neja ta ware masa fili mai faɗin hekta 500 domin gudanar da aikin.
Shugaban kamfanin, Raj Gupta, ne ya bayyana hakan yayin bikin aza harsashin ginin aikin da kuma miƙa filin ga Kamfanin ƙarafa na Abuja Steel Mills Limited, reshen kamfanin African Industries Group, a wani taro da aka gudanar a Abuja a ƙarshen mako.
Gupta ya ce wannan tallafi da gwamnatin jihar ta bayar zai sanya Nijeriya cikin manyan ƙasashen duniya a fannin masana’antar ƙarfe da kuma makamashin da ake sabuntawa.
Ya bayyana cewa kamfanin, wanda ya shafe fiye da shekaru 50 yana gudanar da harkokinsa a Nijeriya, yana kallon wannan sabon faɗaɗa a matsayin wata babbar hanya ta bunƙasa rayuwar al’umma da ƙarfafa tattalin arziki.
A cewarsa, manufar aikin ba wai samar da masana’antu da ayyukan yi kaɗai ba ce, har ma da kawo ci gaba da inganta rayuwar jama’a.
“Wannan aiki na iya zama mafi girma a yankin Afirka da ke kudu da Hamadar Sahara, wanda zai sanya Nijeriya cikin taswirar duniya ta masana’antar ƙarfe da kuma makamashin da ake sabuntawa,” inji Gupta.
A nasa jawabin, Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare masu zurfi a fannin samar da lantarki domin ƙarfafa masana’antu da bunƙasa tattalin arziki.
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, saboda jajircewarsa wajen jawo hannun jarin masu zaman kansu domin bunƙasa tattalin arzikin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Ministan ya ce gwamnati na aiki tuƙuru wajen magance matsalolin da suka sa lantarki ya zama wani abin takaici ga jama’a maimakon ya zama ginshiƙin haɓakar tattalin arziki.
“Mun himmatu wajen samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da za su tabbatar da nasarar irin waɗannan manyan ayyuka,” inji shi.
Shi ma Ministan Raya Masana’antar ƙarafa, Yarima Shuaibu Audu, ya bayyana cewa aikin kamfanin Abuja Steel Mills mai amfani da makamashin hasken rana zai taimaka wajen cimma burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gina tattalin arzikin Nijeriya da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.
A cewarsa, African Industries Group ya zuba jarin biliyoyin daloli a Nijeriya tare da bayar da gudunmawa mai yawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Tun da farko, Gwamna Bago ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa ita ce samar da juyin juya hali a ɓangaren masana’antu, wanda hakan ne ya sa aka ware filin domin aiwatar da wannan aiki.
Ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa na shirin ware ƙarin hekta 200,000 domin jawo sababbin masu zuba jari da tabbatar da ɗorewar ci gaban masana’antu a jihar. “Burinmu na gina sabuwar Jihar Neja na ƙara zama gaskiya a kowace rana,” inji gwamnan.
Bago ya kuma buƙaci masu zuba jarin da su ba mazauna jihar fifiko wajen samar da ayyukan yi domin inganta rayuwarsu.
A nasa ɓangaren, Karamin Ministan Masana’antu, Sanata John Enoh, ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da sabuwar Manufar Masana’antu ta ƙasa, yana mai cewa cigaban tattalin arzikin Nijeriya ya dogara ne sosai da yadda ɓangaren masu zaman kansu zai aiwatar da manufofin ci gaba.
Ya yabawa aikin masana’antar ƙarfen, yana mai cewa zai taimaka wajen rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje tare da samar da dubban ayyukan yi ga matasa.
“Gwamnati ba za ta iya cimma nasarar ƙara yawan samar da kayayyaki ba sai da irin waɗannan manyan ayyuka. Abin da ake buƙata shi ne samarwa da masana’antu,” inji Enoh.
