Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mahukunta a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara sun dakatar da wani malami daga aiki bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yana dukan wasu ɗalibai da ke karatun shiga jami’a na IJMB a harabar makarantar.
A cikin bidiyon, an ga ɗaliban suna durƙushe tare da ɗaga hannayensu yayin da malamin ke dukan su da bulala a tafin hannu. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi Allah-wadai da amfani da hukuncin duka a cibiyoyin ilimi.
Shugaban ƙungiyar ɗaliban Nijeriya, Akinteye Babatunde, ya ce abin da ya faru ba abin amincewa ba ne, yana mai cewa akwai hanyoyin ladabtar da ɗalibai ba tare da amfani da duka ba.
A wata sanarwa da jami’ar ta fitar ta hannun jami’ar hulɗa da jama’a, Halimat Garba, ta bayyana cewa mutanen da aka gani a bidiyon ba daliban Kwara Poly ba ne, sai dai daliban shirin IJMB da suka makara wajen zuwa jarabawarsu.
Makarantar ta ce ko da yake ba a tabbatar da dalilin da ya sa malamin ya aikata hakan ba, amma ta yi tir da abin, tana mai jaddada cewa ba ta amince da duk wani nau’in cin zarafi ko hukuncin duka a matsayin hanyar ladabtarwa.
Sanarwar ta kara da cewa an dakatar da malamin daga aikinsa har sai an kammala binciken da ake yi kan lamarin.
Makarantar ta tabbatar wa jama’a cewa tana gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
