Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta shimfiɗa tubalin Nijeriya sabuwa wadda za ta amfani kowa ta hanyar samar da ci gaba da walwalar al’umma.
Tinubu, wanda shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya wakilta, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da aikin gina tashoshin gefen hanya a Abuja.
Ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara cikin shekaru uku da suka gabata sun kasance masu wahala, amma sun zama dole domin gyara tattalin arziki da bunƙasar ababen more rayuwa.
A cewarsa, an fara ganin sakamakon gyare-gyaren ta hanyar gina hanyoyi, gadoji, layukan dogo da gidaje a sassan ƙasar.
Tinubu ya ce idan an kammala sabbin hanyoyin, za su rage cunkoson ababen hawa da sauƙaƙa zirga-zirgar mazauna yankunan Dutse, Gudu, Gaduwa da Duboyi da kewaye.
Ya kuma yaba wa Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan yadda yake aiwatar da ayyukan raya birnin cikin sauri.
A nasa jawabin, Wike ya ce za a kammala aikin kafin Zaɓen 2027, yana mai gargaɗin masu mamaye filayen gwamnati da su daina gine-gine a kan hanyar da aka ware domin aikin.
