JAMB ta soke shirye-shiryen digiri a kwalejojin ilimi bayan maida NCE hanyar shiga

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB) ta sanar da kawo ƙarshen ɗaukar ɗalibai cikin shirye-shiryen digiri da Kwalejojin Ilimi ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar jami’o’i, lamarin da ya kawo babban sauyi a tsarin horas da malamai a Nijeriya.

Sabon tsarin ya tanadi cewa takardar shaidar karatu daga makarantar horar da malamai , wato Nigeria Certificate in Education (NCE) ce kaɗai za ta kasance hanyar shiga Kwalejojin Ilimi daga shekarar karatu ta 2026/2027.

An bayyana wannan mataki ne a cikin sabbin ƙa’idojin rajistar NCE da ND Agric da ofishin Shugaban Hukumar JAMB ya fitar a watan Yunin 2026.

A ƙarƙashin sabon tsarin, JAMB ta bayyana ƙarara cewa ba za a sake karɓar ɗalibai cikin duk wani shirin digiri da ake gudanarwa ta hanyar haɗin gwiwa a kowace Kwalejin Ilimi ba daga shekarar karatu ta 2026/2027.

Hakazalika, hukumar ta hana ɗaukar ɗalibai kai tsaye zuwa matakin 100 ko 200 a Kwalejojin Ilimi, inda ta jaddada cewa duk masu neman shiga dole ne su bi ta hanyar shirin NCE.

“Daga shekarar karatu ta 2026/2027, ba za a sake karɓar ɗalibai zuwa matakin 100 ko 200 a kowace Kwalejin Ilimi ba. Duk masu shiga za su bi ta hanyar NCE,” inji hukumar.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen wata hanya da dubban ɗalibai suka dade suna amfani da ita wajen samun digiri ta hanyar Kwalejojin Ilimi masu alaƙa da jami’o’i, tsarin da ya shafe shekaru da dama yana gudana a Nijeriya.

Sabon tsarin zai shafi dubban masu neman gurbin karatu da suka zaɓi shirye-shiryen digiri a Kwalejojin Ilimi masu alaƙa da jami’o’i a zangon neman guraben karatu na shekarar 2026.

Domin rage tasirin sauyin ga waɗannan ɗalibai, JAMB ta ba su wasu hanyoyin mafita. Masu neman shiga ta hanyar shigar kai-tsaye, wato Direct Entry za su iya sauya makaranta ba tare da biyan kuɗi ba, ko kuma a mayar da su zuwa jami’ar da ke kula da shirin digirin da suka nema, ko kuma a ɗaga makarantar da suka zaɓa a matsayi na biyu zuwa matsayi na farko.

Haka kuma, masu neman shiga matakin 100 ta hanyar jarrabawar UTME waɗanda suka zaɓi Kwalejojin Ilimi domin karatun digiri za su iya sauya makaranta, ko su ɗaga zaɓinsu na biyu zuwa na farko, ko kuma a mayar da su cikin shirin NCE na kwalejin da suka zaɓa.

By ukarofi

Leave a Reply