Daga MU’AZU HARDAWA a Bauchi
Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar da umarnin rufe Masallacin Ibadurrahman da ke Unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi sakamakon rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin kwamitin gudanarwar masallacin da limaminsa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kulle masallacin, Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya ce an ɗauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin jihar da kuma sahalewar kotu domin kauce wa yiwuwar tashin hankali da ka iya janyo asarar rayuka ko jikkata mutane.
Ya bayyana cewa rikicin ya kwashe kusan shekaru uku yana gudana tsakanin shugabannin masallacin da limamin, kuma an kai lamarin kotuna daban-daban ba tare da an samu mafita mai ɗorewa ba.
A cewarsa, Hukumar Shari’ar Musulunci ta shiga tsakani tun shekarar 2023 inda aka yi sulhu tare da shimfiɗa ƙa’idojin zaman lafiya, amma bangarorin sun kasa mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma.
Barrista Aminu ya ce a wani lokaci ma an dakatar da limamin tare da naɗa wasu ma’aikata domin gudanar da harkokin ibada na tsawon sama da wata guda. Sai dai bayan dawo da shi bakin aikinsa, rikicin ya sake kunno kai.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rufe masallacin ne bayan an samu rahotannin cewa rikicin ya fara ɗaukar sabon salo wanda ka iya kaiwa ga arangama tsakanin bangarorin.
“Ba za mu bari tarihi ya maimaita kansa ba. A baya an taɓa samun rikicin masallaci a Bauchi wanda ya yi sanadin asarar rayuka. Saboda haka gwamnati ta ga ya dace ta ɗauki matakin kariya kafin lamarin ya ta’azzara,” in ji shi.
Kwamishinan ya jaddada cewa duk da kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowa ’yancin gudanar da addininsa, gwamnati na da ikon ɗaukar matakan kariya idan akwai barazanar rashin zaman lafiya.
Ya kuma yi gargadin cewa duk wanda ya karya umarnin rufe masallacin ko ya yi yunƙurin shiga cikinsa ba tare da izini ba zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Barrista Aminu ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da mutunta doka har zuwa lokacin da za a samu cikakkiyar maslaha da warware rikicin.
