Nijeriya za ta kara da Tunisiya, Uganda da Tanzaniya a rukunin AFCON

Spread the love

Najeriya za ta fafata da ƙasashen Tunisiya, Uganda, da Tanzaniya a gasar cin kofin Afrika (AFCON) na shekarar 2025, wanda za a fara a watan Janairu a Morocco.

A yayin bikin raba rukuni da aka gudanar a ƙasar Morocco a ranar Litinin, 27 ga Janairu, 2025, Najeriya ta samu gurbi a Rukunin C tare da sauran ƙasashen uku.

Bikin raba rukunin ya samu halartar manyan baƙi da dama, ciki har da kocin tawagar Morocco, Walid Regragui, tsohon koci Tarik Sektioui, tauraron ƙwallon ƙafa Marouane Chamakh, shugaban FRMF Fouzi Lekjaa, shugaban CAF Patrice Motsepe, da wasu fitattun mutane daga nahiyar Afrika.

A wannan karo, ƙasashen 24 ne za su fafata don neman ɗaukaka a gasar, wanda ke tabbatar da cewa za a samu manyan wasanni masu cike da kishi da kuma ƙwarewa.

An fitar da rukunin ƙasashen da za su fafata, inda aka samu rukuni shida kamar haka:

Rukunin A: Morocco, Mali, Zambia, Comoros
Rukunin B: Masar, Afirka ta Kudu, Angola, Zimbabwe
Rukunin C: Najeriya, Tunisia, Uganda, Tanzaniya
Rukunin D: Senegal, DR Congo, Benin, Botswana
Rukunin E: Aljeriya, Burkina Faso, Equatorial Guinea, Sudan
Rukunin F: Ivory Coast, Kamaru, Gabon, Mozambique

Wannan gasar za ta ba da damar ganin kwallon ƙafa ta Afrika a mafi kyawunta, tare da fatan Najeriya za ta yi nasara a fafatawar da ke gabanta.

By ukarofi