
Daga BELLO A. BABAJI
Hedikwatar rundunar ƴan sandan Nijeriya a Abuja, ta musanta kama Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin-Gado.
Ta ce kaɗai abinda ta yi shi ne gayyatar sa zuwa wajenta bisa wani ƙorafi da aka shigar akansa.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a inda ya ce gayyatar na ɗaya daga cikin ƙa’idojin bincike don warware matsalar.
Ya kuma musanta batun kama Rimin-Gado biyo bayan zargin hukumar ƴan sanda da aka yaɗa na cewa ta yi.
Ya ce ganin yadda doka ta tanadar da kuma kasancewar sa ɗan ƙasa na gari, ya sanya Muhuyi amsa gayyatar ƴan sandan a ƙoƙarinsa na ba su haɗin kai.
Haka kuma rundunar ta ce duk wani bayani da ke nuna cewa kama shugaban hukumar aka yi, to batu ne mai cike da ruɗani da kawar da mutane daga haƙiƙanin abinda ya faru, ya na mai kira ga gidajen jaridu da su kasance masu yaɗa labarai na gaskiya da adalci, ba ababen da za su haifar da cecekuce ba.
Har’ilayau, kakakin ya ce rundunar za ta cigaba da ƙoƙarin kiyaye doka da oda da kuma bin ƙa’idojin gudanar da bincike acikin al’umma.
