
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta fitar da hasashen samun mamakon ruwan sama da tsawa a sassa da dama na faɗin Nijeriya daga Litinin zuwa Laraba, tana mai gargaɗin samun iska mai ƙarfi gabanin tsawa a wasu yankuna.
NiMet ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, inda ta shawarci mazauna yankunan da ta zayyano da su ɗauki matakan kariya yayin da ake tsammanin matakai daban-daban na ruwan sama a sassan ƙasar.
A ranar Litinin, hukumar ta ce akwai yiwuwar samun tsawa da matsakaicin ruwan sama a jihohi Taraba da Kebbi. Ta ce, za a samu hadari da tsawa a rarrabe da kuma matsakaicin ruwan sama a Arewa maso Gabas da jihohin Kaduna, Taraba da Kebbi a yammacin ranar.
A shiyyar Arewa ta tsakiya, za a samu tsawa da yayyafi a sassan jihar Neja a sa’o’in safiya. Sai kuma yayyafi da rana da kuma yammacin a sassan shiyyar.
NiMet ta yi hasashen haɗari a sassan kudancin Nijeriya a safiyar Litinin a jihohin Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom da Kuros-Riba. Sai kuma hadari da yayyafi a rana da yammacin ranar.
A ranar Talata kuwa, NiMet ta yi hasashen ɓurɓushin hadari a arewacin Nijeriya da safe. Sai kuma hadari da yayyafi a Taraba. Daga bisani a rana ko yamma, za a samu hadari da yayyafi a sassa da dama na Arewa. Matsakaicin ruwan sama ake sa ran samu a sassan Abuja, Neja da Filato a lokacin.
A kudanci, ta yi hasashen hadari da yayyafi da safe a sassan Ibonyi, Inugu, Abia da Kudu maso Kudu.
Sai kuma Laraba, inda hukumar ta ce ana sa ran hadari a arewaci tare da matsakaicin ruwan sama a jihohi da dama a safiya. Jihohin sun haɗa da Borno, Bauchi, Gombe, Kaduna, Adamawa da Taraba. NiMet ta kuma ce za a samu tsawa da matsakaicin ruwan sama daga bisani a ranar. A jihohin arewa ta tsakiya za a samu hadari a safiya da tsawa da yayyafi a sassan Abuja, Filato, Neja da Nasarawa. Haka ma a kudancin ƙasar.
Akan haka ta shawarci al’umma da su ɗauki matakan kariya wajen kula da lafiyarsu a halin tafiye-tafiye da zaman gida yayin lokacin musamman ganin yadda damina ke bankwana a sassan ƙasar.
