Hon Sani Liti Yan Kwani ya rasu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Allah yayiwa Hon Sani Liti Yan Kwani rasuwa bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Marigayi Sani Liti ɗan asalin ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina ya taɓa rike muƙamin shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokoki na Katsina.

Haka kuma ya riƙe muƙamin shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Katsina kafin daga nan ya koma mai sharhi a harkokin siyasa da na yau da kullum.

Ya rasu ya bar mata uku da ya’ya 26 ,tuni akayi jana’izarsa a gidansa.

By ukarofi

Leave a Reply