Shettima ya isa New York don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa birnin New York ta ƙasar Amurka domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu da jagorantar tawagar Nijeriyar a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 UNGA.

An bayyana haka ne a wata sanarwa da aka fitar a yau Litinin, inda mataimakin shugaban ƙasar yake cewa hada-hadar Nijeriya a taron za su fi karkata ne ga maslahar ƙasar, ƙoƙarin warware muhimman batutuwan difulomasiyya, da kuma kiran Shugaba Tinubu na a samar da gyare-gyare ga cibiyoyin duniya domin dacewa da halin tattalin arziƙi da yanayin ƙasashe.

Shettima ya jagoranci tawagar ne, wadda ta haɗa da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal; ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati. Za a gudanar da taron a ranakun 22 zuwa 28 ga Satumba, 2026 a ƙarƙashin taken, “Restoring trust, managing transformation: A United Nations that delivers for all.”

Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai dawo Nijeriya da zarar an kammala taron da wasu harkokin gwamnati a New York. Shettima dai zai yi jawabin Nijeriya ne kan matsayarta game da muhimman al’amuran duniya tare da tasirinsu ga ci-gaban ƙasa, zaman lafiya da tsaro da kuma haɗin kai tsakanin ƙasashe da dai sauransu.

Yayin da ya sauka, Shettima ya samu tarba daga Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Haɗejia; Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu; Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim; Ministan Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Dele Alake; Babban Wakilkn Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, da wasu manyan jami’an gwamnati da jami’an difulomasiyya.

By Babaji

Leave a Reply