Sojoji sun kama ɗan bindiga da ake alaƙantawa da kisan marigayi Janar Rabe

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar soji ta Operation FANSAN YAMMA, tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai sun kama manyan kwamandojin wata dabar ‘yan ta’adda da ta shahara wacce ke da alaƙa da sace wa tare da kashe Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) a Jihar Katsina.

Wani majiyar soji a Gusau, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa, aikin da aka gudanar a ranar Lahadi ya kai ga kama wasu manyan mambobin ƙungiyar da ke aiki ƙarƙashin jagorancin wani mai suna Kachalla Maha.

A cewar majiyar, cikin waɗanda aka kama akwai wani babban kwamanda mai suna Samagi, wanda aka bayyana a matsayin muhimmin mutum a tsarin gudanar da ayyukan ƙungiyar.

Ana kallon kama waɗannan manyan kwamandoji a matsayin babban ci gaba a yaƙin da ake yi na tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma karya lagon tsarin jagorancinsu a yankin Arewa maso Yamma.

Ana zargin waɗannan mutane da taka muhimmiyar rawa wajen sace mutane, kisan kai, da sauran hare-haren tashin hankali da ake dangantawa da ƙungiyar Kachalla Maha a sassa daban-daban na yankin.

Aikin, wanda ya ƙunshi sojojin Operation FANSAN YAMMA da ‘yan sa-kai na yankin, ya nuna muhimmancin samun ingantattun bayanai daga mazauna yankin da kuma haɗin gwiwar al’umma wajen bibiyar ‘yan ta’addar da ke aiki a wurare masu wuyar shiga.

Wani shugaban ‘yan sa-kai mai suna Mamara ya bayyana cewa, kama Samagi da sauran manyan mambobin ƙungiyar na iya bai wa hukumomin tsaro muhimman bayanai game da shugabancin qungiyar, hanyoyin gudanar da ayyukansu, maɓoyarsu, hanyoyin samun kayan aiki, da kuma waɗanda ke ba su taimako.

Kisan Manjo Janar Rabe (mai ritaya) ya ƙara haifar da damuwa game da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma barazanar da suke haifarwa ga jami’an tsaro da fararen hula a yankin Arewa maso Yamma.

Jami’an tsaro na ci gaba da tsaurara ayyukan yaqi da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a wuraren da aka gano suna ɓoye wa, da nufin hana su walwala da kuma raunana ƙarfinsu na kai hare-hare ko sace mutane.

Majiyoyi sun ce ana sa ran waɗannan sabbin kamun za su taimaka wajen tattara bayanai da kuma gano sauran mambobin ƙungiyar da alaƙar da ke tsakaninsu da hare-haren da aka taɓa kaiwa a baya.

Ana sa ran za a ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin domin tantance takamaiman rawar da kowannensu ya taka a ayyukan ƙungiyar Kachalla Maha da kuma hannunsu a wasu lamuran tashin hankali a Jihar Katsina da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

By ukarofi

Leave a Reply