NNPC ta ƙara kuɗin litar man fetur

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kamfanin NNPCL ya ƙara farashin man fetur a gidajen sayar da shi, bayan da matatar Dangote ta yi gyaran farashi. Wannan sauyi ya jawo ƙarin kuɗin lita na fetur a kasuwa.

Binciken kasuwa da aka gudanar a Abuja ya nuna cewa farashin fetur a gidajen NNPCL ya tashi daga N1,295 zuwa N1,364 kan kowace lita, wanda ke nuna karin N69. An fara aiwatar da sabon farashin a wurare daban-daban kamar Gwarimpa, Kubwa Expressway, Wuse Zone 6 da kuma Zone 4.

Sauran gidajen mai kamar MRS Oil Nigeria da BOVAS Group suma sun kara farashinsu zuwa tsakanin N1,365 zuwa N1,370 kan kowace lita. Wannan karin ya biyo bayan matakin da matatar Dangote ta ɗauka na ƙara farashin sayarwa zuwa N1,275 daga N1,200, sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya zuwa sama da dala $115 kan kowace ganga.

By ukarofi