Daga USMAN KAROFI
Wakilin jaridar Blueprint a Zariya, Mohammed Habib, ya yi rashin ɗansa guda ɗaya, Mubarak Habib.
Marigayin mai shekaru 29 ya rasu a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a yammacin ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mahaifin cikin alhini ya ce, “Na rasa ɗana guda daya. Yana da shekaru 29.”
Habib ya bayyana cewa marigayin ya yi jinya na wasu kwanaki kafin rasuwarsa da misalin tsakar rana.
Labarin rasuwar tasa ya jefa ‘yan uwa, abokai da abokan aiki cikin jimami.
Masu jaje sun ci gaba da tururuwa zuwa ga iyalan mamacin, suna yi masa addu’ar samun rahama tare da roƙon Allah ya bai wa iyalan haƙurin jure wannan rashi.
