NNPC zai kasance babban abokin cinikin matatar Ɗangote – Jami’in Gudanarwa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An yi hasashen cewa kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL ne zai zama babban abokin ciniki yayin da matatar man fetur ɗin Dangote ke shirin fara fitar da mai.

Matatar man Dangote ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon ƙarancin zanyen mai a baya-bayan nan, inji wani jami’in gudanarwa a ranar Litinin.

Matatar mai da ta kai dala biliyan 20 a wajen birnin Legas, wanda hamshaƙin attajirin nan ɗan Nijeriya, Aliko Dangote ya gina, ta fara aiki ne a watan Janairu tare da samar da man da har zai isa a fitar da shi ƙasashen waje.

Sai dai bai bayyana takamaiman lokacin da man fetur ɗin zai afka kasuwannin ƙasar ba.

Edwin ya ce, kamfanin mai na ƙasa NNPC, mai shigo da mai a Nijeriya shi kaɗai zai sayi man fetur ɗinsa.

“Idan babu wanda ke sayen sa, za mu fitar da shi zuwa ƙasashen waje kamar yadda muke fitar da man jiragenmu da dizal,” inji Edwin.

Isar da man fetur a kasuwannin Nijeriya zai sauƙaƙa fafutukar da kamfanin na NNPC ke yi na wadata kasuwannin cikin gida. 

Kamfanin dai na cikin matsane ne da basussukan dala biliyan 6 ga dillalan mai domin samar da su tun watan Janairu.

Hakan dai ya shafi yadda take samar da kasuwannin cikin gida inda layukan mai ke ci gaba da wanzuwa tun watan Yuli.

Farashin ya yi tashin gwauron zaɓi da kashi 45 cikin 100 daga farashin da ya kai Naira 617 (dala 0.3942) da aka bayyana bayan an cire tallafin a bara.

“Labarin cewa Dangote yana sarrafa man fetur ba zai iya zuwa a wani lokaci mai muhimmanci ba idan aka yi la’akari da bayanin da NNPC ya yi game da matsalolin da yake fuskanta wajen samar da wadatar da ake shigowa da su daga waje saboda matsalar kuɗi,” inji Clementine Wallop, darektan, yankin kudu da hamadar Sahara a kan harkokin siyasa, Horizon Engage.

Ta ce hakan ya sanya ayar tambaya kan yadda kamfanin na NNPC zai tafiyar da sayen man daga Dangote, kuma ya nuna gaskiya a cikin ayyakansa.

By ukarofi