NNPCL ya sallami manyan jami’an da suka yi aiki ƙarƙashin Mele Kyari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL ya sallami manyan jami’an da suka yi aiki tare da tsohon shugabansa, Mele Kyari.

Daga cikin su akwai tsohon shugaban Hukumar Kula da zuba Hannun-jari a Man Fetur ta Ƙasa (NAPIMS) Bala Sunyi da Ibrahim Onoja, daraktan Matatar Kaduna da Lawal Sade.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, aƙalla ma’aikata 200 lamarin ya shafa, wanda ke nuna yadda kamfanin ya yi gagarumin garambawul.

Hakan ya kuma nuna yadda aka samu ƙarin adadi na mata da suka samu manyan muƙamai a kamfanin, waɗanda daga ciki akwai Maryam Idrisu a matsayin Darakta Manaja ta ɓangaren Kasuwanci da Obioma Abangwu a matsayin Babbar jami’ar harkokin manyan jami’ai.

A ranar 2 ga watan Afrilun 2025 ne aka sallami manyan daraktocin kamfanin, lamarin da ya kai Bayo Ojulari maye gurbin Mele Kyari.

By Babaji