Zamfara: ‘Yan ta’adda sun kashe limami da ‘ya’yansa biyu bayan watanni biyu a tsare

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da babban limamin masallacin Maru dake hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara Alhaji Salisu Suleman, rahotanni sun nuna cewar sun kasheshi tare da ‘ya’yansa maza biyu da suka yi garkuwa da su watanni biyu da suka gabata.

Marigayi Malam Salisu a ranar 13 ga watan Fabrairun wannan shekara aka yi garkuwa da shi tare da matansa biyu da ‘ya’yansa bakwai a gidansa bayan wani samame da ‘yan bindiga suka kai a garin na Maru.

Ɗaya daga cikin surikansa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Blueprint Manhaja ta wayar tarho sun samu rahoton kashe limamin ne da ‘yayansa biyu bayan karɓar kuɗin fansa Kuma suka ƙi sakin marigayi Malam Salisu da ‘ya’yan nasa biyu a yau Talata.

“Yau 29 ga watan Afrilu, mun samu rahoton cewa ‘yan bindiga sun kashe Malqm Salisu da ‘ya’yansa biyu sama da wata ɗaya da ya gabata tun cikin watan Ramadan.

“Marigayi surikina ne kuma mun yi rashin uba mai tawali’u kuma mai tsoron Allah”. Ya ƙara da cewa

A cewarsa, an gudanar da Sallah janazar marigayi Malam Salisu da ‘ya’yansa biyu watau (Salatul Ga’ib,) a yau a garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara.

By ukarofi