Jaridar Neptune da YFM za su horar da ‘yan jarida a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu

Kamfanin Neptune Network Nigeria Limited (NNNL), mai buga jaridar Neptune Prime a Turanci da Hausa, tare da tallafin kungiyar ‘Yobe First Movement (YFM), za su gudanar da taron horarwa na yanki kan dabarun yaɗa labaru, wanda zai gudana a garin Potiskum, dake jihar Yobe, ranar Laraba.

Wannan bayani ya na ƙunshe ne a wata sanarwa ga manema labarai mai ɗauke da sa-hannun mawallafin/shugaban kamfanin NNNL, Malam Hassan Gimba, inda ya ce, taron zai ƙarfafa ƙwarewa da sanin makamar aikin jarida domin faɗakar da jama’a da kuma yadda ake amfani da shafukan sada zumunta don isar da saƙo.

A cewarsa, hakan zai tabbatar da cewa ya horas da mahalarta taron dabaru da samun ƙwarewar rubuce-rubucen da suka shafi abubuwan da suke faruwa na al’ammuran yau da kullum, waɗanda suka shafi manufofin gwamnati.

Horon, wanda ya ƙunshi ƙungiyoyin al’umma 20 daga ƙananan hukumomin Potiskum, Fika, Fune, da Nangere dake Jihar Yobe, wanda za a gudanar a garin Potiskum.

Har ila yau kuma, wannan horon zai amfanar a matsayin samfuri na farko, wanda masu shirya taron za su wajen zaƙulo ƙarin wasu ƙungiyoyi daga sauran sassan jihar, nan gaba.

Ƙwararru da za su gudanar da ayyukan bayar da horon sun haɗa da Dokta Ahmed Mohammed Bedu, ƙwararre a fannin sadarwa, kuma tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa a Jihar Yobe (NUJ), kuma malami a Jami’ar Maiduguri; Dokta Saleh Mari Maina, ƙwararren ɗan jarida kuma malami a cibiyar ci gaba mai ɗorewa, Jami’ar Abuja da Jami’ar Bayero (BUK) da Jami’ar Baba Ahmed, duka a Kano.

Sauran su ne Malam Abubakar Ahmed, tsohon mataimakin darakta a Kamfanin Dillancin Labaru (News Agency of Nigeria- (NAN), da Dokta Furera Bagel, malama a fannin ilimin harshe a Jami’ar Jihar Bauchi.

By ukarofi