
Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin mutane 15 ne ƴan ta’adda suka kashe a yayin wani zaman makoki da garkuwa da wasu a Ƙauyen Kwaple dake kusa da Ƙaramar Hukumar Chibok a Jihar Borno.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Litinin, a lokacin da ƴan zaman makokin suke jimamin rashin ɗaya daga cikin ƴan ƙauyen.
A yayin tabbatar da lamarin, Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Modu Mustapha ya ce maharan sun farmaki al’umma ne a lokacin zaman makokin inda suka kashe mutane da dama.
Wani shaida da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, aƙalla mutane 15 ne suke kashe yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama.
Ya kuma ce, sun ƙone cocin EYN da wasu gidaje biyar gami da wasu kadarori.
