DSS na fuskantar matsin lamba don sakin Baruten da aka kama da makamai a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Ƴan sandan Farin kaya, DSS ta na fuskantar matsi biyo bayan cafke wani bature bisa laifin fasa-ƙaurin bindigu ƙirar AK47 guda 50 a jihar Delta.

Jaridar EmergencyDigest ta ce, ana matsa wa hukumar ne kan kama baturen mai suna Manjo Micah Polo da hannu a laifin jigilar makaman da aka kama a makon da ya gabata a jihar.

A ranar Juma’a ne jami’an DSS suka kama Manjon a Legas, a lokacin da ya yi yunƙurin ficewa daga Nijeriya.

Ana zargin sa ne da alaƙa da wani basarake mai suna Ogiame Atuwatse III na yankin Warri.

Hakan ya biyo bayan ƙwato bindigu ƙirar AK47 guda 50 da wasu alburusai 3,000 ne a yayin wani atisaye da jami’anta a jihar suka gudanar a yankin Asaba. A lokacin ne aka kama waɗanda Manjo Polo ya ke aiki tare da su.

A saboda haka ne ya zama wanda ake zargi da hannu a shigowa da makaman ta haramtattun hanyoyi zuwa Nijeriya.

A ranar Litinin ne shaidu daga SSS suka bayyana cewa, an samu saƙonni daga ofishin gwamnan jihar da wasu mataimakan Olun na Warri da ke neman a sako baturen.

Sun ce, an yi haka ne saboda ana ganin DSS ba za ta bari batun ya tafi a kara-zube ba la’akari da yadda halin tsaro taɓarɓare a Nijeriya.

By Babaji