Yadda Aisha Achimugu ta ƙi cin abinci a hannun EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shahararriyar Attajira, A’isha Achimugu, ta ƙi amincewa da cin abinci a yayin da ta ke hannun jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC.

A ranar Talata ne tawagar shari’arta ƙarƙarshin jagorancin Chikaosolu Ojukwu (SAN), ta sanar da cewa an kama Attajira Aisha ne da misalin ƙarfe 5 na asuba a Filin Jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Tun a watan Maris ne EFCC ta sanar da neman Attajirar ruwa-a-jallo sakamakon zargin ta da hannun a aikata manyan laifuka da suka haɗa da badaƙalar wasu kuɗaɗe.

Haka kuma, Babbar Kotun Tarayya ta umarci A’isha Achimugu da ta kai kanta ga hukuma a ranar Talata ta kuma je kotun a ranar Laraba.

Saidai, tawagar alƙalan nata ta ce Achimugu ta zo tun daga London don amsar gayyatar hukumar, inda gabannin haka ne jami’anta suka kama ta.

Lauya Ojukwu ya kuma ce, ta sanar da Babbar Kotun cewa za ta je amsa gayyatar hukumar a ranar Talata bisa tuhumar da ake mata.

By Babaji