
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Farouk Joɓe, ya koka kan yadda kishin ƙasa yayi rauni a tsakanin ƴan Nijeriya.
Ya nuna takaicinsa ga yadda ƴan ƙasa suka yi watsi da tarihinsu da kishin ƙasa wanda hakan ya jefa mutane da dama cikin halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa.
Mataimakin gwamnan, wanda shi ne babban baƙo wajen taron da Hukumar Gyaran Aƙida ta Ƙasa (NOA) ta shirya a Katsina, ya ce Nijeriya na da arziƙin ƙasa da yawan al’umma wanda ita kanta al’ummar arziƙi ce.
A nasa jawabin, Shugaban NOA, Mista Lanre Issa_onilu wanda ya samu wakilcin Muntari lawal Tsagem, ya bayyana muhimmancin farfaɗo da aƙidojin son ƙasa da mutunta ƙasa tare da son ƙasa a gaba da dukkan al’amura.
“Cusa aƙidar ƙasa a zukatan ƴan ƙasa da suka haɗa da; alamomin kasa, tutar ƙasa, tambarin ƙasa da sauransu sune muhimman ayyukan da hukumar tasa a gaba yanzu.”
Taron ya samu halartar jami’an tsaro na ƴan sanda da jami’an Civil Defence da na shige da fice.
Akwai kuma wakilan sarkin Katsina da na Daura da manyan jami’an gwamnatin Katsina.
