
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya bayan shafe makonni ya hutunsa na shekara.
Mai taimaka masa, Dada Olusegun ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya iso Nijeriya, inda ya ke masa maraba da dawowa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar.
Tinubu ya iso Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe ne da ke Abuja da dare bayan ƙarewar lokacin hutun.
